Jiya Laraba ne aka bude taron shugabannin masana'antu da kasuwanci na kungiyar hadin gwiwa ta nahiyar Asiya da yankin tekun Pasific wato APEC na shekarar 2017 a birnin Da Nang da ke tsakiyar kasar Vietnam. A yayin wannan taro, za a tattauna kan sabon yanayin da ake ciki na dunkulewar kasashen duniya duniya baki daya, dunkulewar shiyya-shiyya ta fuskar tattalin arziki, karfin kamfanoni kanana da matsakaita na yin takara da dai makamantansu.
An labarta cewa, shugabanni fiye da dubu 2 daga kamfanonin Asiya da yankin tekun Pasific za su halarci taron na kwanaki 3, ciki had da wasu fiye da 300 wadanda suka fito daga kasar Sin. (Tasallah Yuan)