in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da uwargidansa sun ziyarci fadar sarakunan kasar Sin tare da Trump da uwargidansa
2017-11-09 11:09:01 cri

A yammacin jiya Laraba ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan suka ziyarci fadar sarakunan kasar Sin dake nan birnin Beijing tare da shugaban kasar Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania Trump wadanda ke ziyarar aiki a kasar ta Sin, yayin ziyararsu, shugabannin kasashen biyu da uwargidansu sun sha shayi tare kana suka kalli nune-nunen da aka shirya musu game da fasahar gyara kayayyakin tarihi, da kayayyaki tarihi masu daraja da aka adana a fadar, daga bisani kuma suka kalli wasan opera a cikin fadar.

Shugaban Amurka Trump ya iso birnin Beijing ne a yammacin jiya, inda ya fara ziyarar aiki a kasar ta Sin, da saukar su a filin jirgin sama Trump da uwargidansa sun nufi fadar sarakunan kasar Sin cikin mota kai tsaye.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan sun jira su a fadar inda suka tarye su, kana suka fara ziyarar tare da kewaya fadar na kusan tsawon sa'o'i hudu.

Da farko, shugaba Xi ya nuna gagarumar maraba da zuwan shugaba Trump, inda ya jaddada cewa, ziyarar da Trump ke yi a kasar Sin tana da babbar ma'ana, ba ma kawai ta jawo hankalin kasashen Sin da Amurka kawai ba, har ma ta jawo hankalin kasashen duniya baki daya, Xi ya kara da cewa, ziyarar za ta haifar da sakamako mai faranta ran mutane kamar yadda ake fata bayan kokarin da sassan biyu suke, kana kamar yadda Trump ya bukace shi, Xi ya yi bayani kan halin da kasar Sin ke ciki wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da kuma muhimman sakamakon da aka samu yayin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 wanda aka kammala ba da dadewa ba.

A nasa bangaren, shugaba Trump ya godewa kasar Sin saboda abubuwan da ta shirya musamman domin ziyararsa, kana ya taya kasar Sin murnar kammalar babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 cikin nasara, Kana ya taya Xi murnar sake zaben sa a matsayin babban sakataren jam'iyya mai mulki ta kasar Sin, ban da haka kuma Trump ya jinjinawa sakamakon da kasar Sin ta samu wajen raya tattalin arziki, tare fatan cewa, ziyarar aikin nasa za ta kai ga samun nasara.

Yayin da shugabannin biyu ke zantawa a dakin shan shayi, Trump ya nuna wa Xi da uwargidansa wani hoton bidiyon jikarsa Arabella tana rera waka da Sinanci, kuma ta karanta wakokin gargajiyar kasar Sin da Sinanci, "Sannunka kaka Xi, sannunki kaka Peng, barka, bari in rera muku wata waka."

Shugaba Xi ya ce, Arabella ta iya Sinnanci sosai, har ta zama tauraruwa a kasar Sin, yana fatan wata rana Arabella za ta zo nan kasar Sin yawon shakatawa.

Daga baya shugaba Xi da uwargidansa Peng sun kai ziyara fadar Taihe da ta Zhonghe da kuma ta Baohe, domin kara fahimtar al'adun gargajiyar kasar Sin wato zaman jituwa. Shugaba Trump ya yi mamakin ganin manyan gine-ginen gargajiyar kasar Sin dake cikin fadar sarakunan kasar Sin, Xi ya bayyana cewa, "Ana kiyaye al'adun gargajiyar kasar Sin yadda ya kamata, kuma har yanzu ana ci gaba da wannan aiki,"

Yayin ziyarar, Trump ya tambaye Xi cewa, ko wannan shi ne ainihin al'adun kasar Sin, Xi ya amsa cewa, haka ne, mu ma ainihin al'ummar kasar Sin ne, gashin kai mai launin baki, fata mai launin rawaye, ana kiran mu da sunan jikokin dabbar dragon.

Daga baya sun je dakin da ake gyara kayayyakin tarihi, inda suka kalli yadda ake aikin gyara kayayyakin tarihi, da kayayyakin tarihi masu daraja da aka baje kolin su. Gaba daya shugabannin kasashen biyu sun jinjinawa hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu biyu a fannin gyara kayayyakin tarihi.

Bayan da suka kammala ziyara a dakin, sai suka je kallon nune-nunen wasan opera a cikin fadar.

Yayin ziyararsu a fadar sarakunan kasar Sin, shugabannin biyu sun yi musanyar ra'ayoyi kan batutuwan da suka fi jawo hankalinsu, misali yadda ake tafiyar da harkokin kasa, da huldar dake tsakanin Sin da Amurka da sauransu.

A daren jiya, shugaba Trump ya rubuta labari na farko a shafin intanet na Twitter, inda a madadin shi kansa da uwargidansa ya nuna godiya ga shugaba Xi da uwargidansa, saboda dadin da ya ji matuka yayin ziyararsa a yammacin jiyan(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China