in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana juyayin rasuwar 'yan kasar 26 a tekun Mediterranean
2017-11-08 10:47:42 cri

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, ta yi matukar nuna juyayi dangane da mutuwar 'yan kasar su 26 a tekun Mediterranean.

Abike Dabiri-Erewa, babbar mashawarciya ta musamman ga shugaban kasar game da 'yan Najeriya dake kasashen waje da kuma hulda da kasashen waje ta bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, matasan da suka gamu da ajalin nasu sun mutu ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta ficewa zuwa ketare domin neman aiki mai tsoka, amma sai suka fada cikin mawuyacin hali, da cutarwa, wasu kuma sun gamu da ajalinsu.

A cewarta, mutuwar wadannan matasa 'yan Najeriya, mafi yawansu mata ne da 'yan mata, ta bayyana cewa, abin takaici ne. Ta ce, dole ne a ci gaba da wayar da kan al'umma dangane da illolin dake tattare da irin wannan tafiya mai matukar hadari.

Abike ta ce, batun yawaitar bakin haure yana neman zama babbar matsala a duniya baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China