in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana na Sin da waje na mai da hankali kan yadda kasashen Sin da Amurka za su kara yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya
2017-11-08 10:39:20 cri

A yau Laraba ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki 3 a kasar Sin. Wasu kungiyoyin 'yan kasuwa da masu masana'antu na kasar Amurka wadanda suke rufawa shugaba Trump baya a wannan ziyara, za su halarci wasu tarukan tattalin arziki da cinikayya tare da takwarorinsu na kasar Sin, inda za su rattaba hannu kan wasu kwangiloli. Sabo da haka, kamfanonin kasar Sin da masana na kasar Sin da na waje suna fatan kasashen Sin da Amurka za su kara yin hadin gwiwa domin cimma nasara tare.

A watan Oktoban bana ne, kamfanin BYD wanda ya yi suna wajen kera motoci masu aiki da sabon makamashi maras gurbata muhalli a nan kasar Sin, ya habaka reshensa a karo na uku da ya kafa a garin Lancaster dake jihar California ta kasar Amurka. Sabon kamfanin kera ababen hawa mai aiki da batura shi ne na farko mai jarin kasar Sin da aka kafa a kasar Amurka, kana kamfanin kera ababen hawa mafi girma da aka kafa a nahiyar Arewacin Amurka. Rahotanni na cewa, a shekarar 2013, kamfanin BYD ya zuba jarin kimanin dalar Amurka miliyan 230 a kasuwar ababen hawa mai aiki da batura. Madam Li Wei, babbar direktar hulda da jama'a ta kamfanin BYD ta bayyana cewa, "Kamfanin BYD na samarwa kasuwar kasar Amurka taimako da goyon baya a fannoni biyu, wato dukkan kayayyakin da kamfaninmu ke samarwa a kasar Amurka kayayyaki ne masu aiki da sabon makamashi marasa gurbata muhalli. Suna ba da gudummawa matuka ga kokarin kare muhallin wurin da lafiyar al'ummar wurin, da kuma samar da yanayin karatu da na rayuwa mai inganci ga zuriyoyin dake tafe. Sannan, yawan ma'aikanta Amurkawa dake aiki a reshen kamfaninmu dake kasar Amurka ya kai kashi 95 cikin dari na jimillar ma'aikatan kamfani. Kawo yanzu, mun dauki Amurkawa fiye da dari 8 don su yi aiki a kamfaninmu dake garin Lancaster."

Batun kara yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya wani muhimmin abu ne ga ziyarar shugaba Trump a kasar Sin. Bangarori daban daban na fatan kasashen Sin da Amurka za su kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya. Madam Li Wei tana fatan kasashen Sin da Amurka za su kara yin hadin gwiwa a fannin ababen hawa mai aiki da sabon makamashi. Madam Li tana mai cewa, "A ganina, ababen hawa masu aiki da sabon makamashi, wani fanni ne mai kyau. Bangarorin biyu za su iya kara yin hadin gwiwa a kai. Alal misali, kafin kamfanin BYD ya shiga kasuwar Amurka, an shafe shekaru 7 ana amfani da ababen hawa masu aiki da sabon makamashi a kasar Sin. Muna da dimbin bayanai game da yadda za a tafiyar da su da gyara da kuma kayayyaki masu inganci. Me ya sa kayayyakinmu suka samu karbuwa a kasuwar Amurka? Sabo da kayayyakinmu suna amfani da sabuwar fasahar da babu irinta a kasar Amurka. Sakamakon haka, a ganina, kasashen biyu za su iya kara yin hadin gwiwa a fannin samar da ababen hawa masu aiki da sabon makamashi."

A kwanan baya, jakada Cui Tiankai na kasar Sin dake kasar Amurka ya bayyana cewa, idan bangaren Amurka ya sassauta sharudan da suke hana fitar da kayayyakin yau da kullum na zamani da jama'a ke bukata zuwa kasar Sin, tabbas za a kara yawan kayayyakin da kasar Amurka za ta fitar zuwa kasar Sin, kuma hakan zai taimaka wa kokarin daidaita matsalar rashin daidaito da ta dade tana kasancewa a tsakanin kasashen Sin da Amurka a fannin cinikayya.

Sannan, a kwanan baya, madam Charlene Barshefsky, tsohuwar wakiliyar cinikayya ta kasar Amurka ta jaddada cewa, bai kamata a aiwatar da manufar kariyar cinikayya ba. Madam Barshefsky tana mai cewa, "A ganina, kasashen Sin da Amurka suna da babban nauyin daidaita harkokin kasa da kasa. Akwai bukatar su bullo da wata huldar moriyar juna a tsakaninsu. Amma manufar kariyar cinikayya tamkar wani abokin gaba ne ga sassa biyu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China