Ministan harkokin addini na kasar Mohamed Aissa shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, masallatai da Limaman kasar sun dauki matakan da suka dace na toshe duk wasu kafofin yada tsattsauran ra'ayin addini a kasar, inda yanzu suke nunawa jama'a tsari da ka'idjojin addinin musulunci na zahiri.
Ministan ya ce, malaman addini suna taka muhimmiyar rawa wajen yada koyarwar addinin musulunci yadda ya kamata, sabanin hanyoyi marasa kyau da kasar ta tsinkin kanta a baya.
Aljeriya dai ta fuskanci ayyukan ta'addanci a shekarun 1990, tun lokacin da kasar ta bullo da matakan yaki da ayyukan ta'addanci a fadin kasar. (Ibrahim Yaya)