in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mu'amala tsakanin shugabannin Amurka da Sin za ta taimaka ga raya dangantaka tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata
2017-11-07 10:34:14 cri

Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Amurka Donald Trump zai kawo ziyara kasar Sin tun daga ranar 8 zuwa 10 ga wannan wata. Gabanin ziyarar da shugaba Trump zai kawo kasar Sin, shugaban kwamitin kula da harkokin dangantaka tsakanin Amurka da Sin na kasar Amurka Stephen Orlins ya yi hira da wakilin gidan rediyon kasar Sin CRI.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai kawo ziyara kasar Sin tun daga ranar 8 zuwa 10 ga wannan wata. Shugaban kwamitin kula da harkokin dangantaka tsakanin Amurka da Sin na kasar Amurka wato NCUSCR Stephen Orlins ya bayyana cewa, ganawar da shugabannin Amurka da Sin za su yi za ta kara musu fahimtar juna da sada zumunta, da cimma daidaito kan manyan batutuwan dake shafar kasashen biyu. Kiyaye mu'amalar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu za ta taimaka wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Mr Orlins ya bayyana cewa,

"Ganawar farko da shugabannin Amurka da Sin suka yi ta samu kyakkyawan sakamako, shugabannin kasashen biyu sun fahimci juna tare da fuskantar kalubale tare. Hirar da shugabannin kasashen biyu su kan yi tana da amfani sosai. Ganawar da za su yi a birnin Beijing na kasar Sin ita ce ganawa ta uku a tsakaninsu. Yana da kyau idan shugabannin kasashen biyu suka ci gaba da ganawa a tsakaninsu"

Mr Orlins ya yi nuni da cewa, tun bayan da sabuwar gwamnatin kasar Amurka ta kama aiki, ana kiyaye mu'amala a tsakanin Amurka da Sin. A watanni shida da suka gabata, an gudanar da zagayen farko na shawarwari tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu sau hudu, inda suka fadada hadin gwiwa a fannonin harkokin diplomasiyya, tattalin arziki da cinikayya, aiki soja, dokoki, tsaron internet, al'adu da kananan gwamnatocin kasashen biyu da dai sauransu. A mataki na gaba, bangarorin biyu za su yi kokarin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma daidaito a gun shawarwarin. A cikinsu, kara hadin gwiwar dake tsakanin kananan hukumomin kasashen biyu da mu'amalar dake tsakanin jama'ar kasashen biyu su ne a kangaba.

Ana sa ran yayin ganawar shugabannin kasashen biyu a wannan karo, za su kara tattaunawa kan manyan batutuwan da suke mai da hankali tare don cimma daidaito a kai, ciki har da batun tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu. Mr Orlins ya bayyana cewa, muddin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a fannin tattalin arziki da cinikayya da nufin samun moriyar juna, ya kamata shugaba Trump ya kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a wannan fanni, da daukar matakai don warware matsalar rashin daidaito kan cinikin dake tsakanin Amurka da Sin. Orlins ya bayyana cewa,

"Game da batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Amurka da Sin, mun ga shugaba Trump zai jagoranci tawagar wakilan ciniki ta kasar Amurka yayin ziyarar da zai kawo kasar Sin, ciki har da manyan shugabannin kamfanonin kasar Amurka fiye da 10, wadanda suke son daddale yarjejeniyoyin tattalin arziki da cinikayya a wannan karo. A don haka bai kamata shugaba Trump ya mai da hankali ga gibin cinikin dake tsakanin Amurka da Sin ba, ya kamata ya yi la'akari da fannoni daban daban yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin kasashe biyu a tattalin arziki da cinikayya."

Orlins ya kara da cewa, Amurka da Sin suna da moriya iri daya da nauyin dake kansu a kokarin da ake a tabbatar da zaman lafiya da samun bunkasuwa da wadata a duniya gaba daya. Orlins ya yabawa muhimmiyar rawar da kasar Sin ta taka kan harkokin kasa da kasa. Orlins ya yi nuni da cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar tana da muhimmanci matuka ga dukkan duniya ciki har da jama'ar kasar Amurka. Orlins ya ce,

"Shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta gabatar tana da ma'ana matuka ga Amurkawa. Kamfanonin kasar Amurka za su amfana ta hanyar shiga a dama da su a cikin shawarar, kana batun kawar da talauci a duniya wani babban nauyi ne da ke wuyan kasashe masu arziki. Kasar Sin ta dauki wannan alhaki. Talauci ya kan haifar ta'addanci. Sin ta gabatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kara zuba jari ga kasashen dake cikin shawarar, da taimakawa kasashen wajen kawar da talauci, wannan zai taimaka wajen kawar da ta'addanci daga tushe. Kuma wannan yana da muhimmanci matuka ga al'umma kasar Amurka." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China