Ana sa ran binciken zai kunshi masana 334, kamar dai yadda shugaban cibiyar nazarin binciken wurare masu sanyi na kasar Sin, kuma jagoran tawagar Yang Huigen ya tabbatar.
Bisa tsarin aikin, tawagar masu binciken za ta kammala tafiyar da ta kai mil kusan 36,000, ana kuma sa ran dawowar ta birnin Shanghai a watan Afrilun shekara mai zuwa.
Binciken kimiyyar karo 34 zai hada da safiyo a matakin farko, game da shirin da ake yi na kafa tashar kasar Sin ta 5 a yankin na Antatika, wadda za ta zamo a yammacin gabar tekun Ross.