A fannin bukatun albarkatun kwadago, kamfanonin kasar sun kara bukatar sabbin ma'aikata a wannan lokaci. Lokacin ya kasance wani lokaci ne da yawan mutanen da suka zabi canja aiki ya ragu, kana an fara karatu a jami'o'in kasar, dalibai sun rage neman aikin yi a lokacin, don haka yawan mutanen da suka nemi aiki a lokacin shi ma ya ragu. Idan aka kwatanta jimillar da ta makamancin lokacin a bara, yawan guraben aikin yi da aka samar ya karu, wannan ya bayyana cewa, ana gudanar da aikin samar da ayyukan yi yadda ya kamata a kasar ta Sin. (Zainab)