in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da Bill Gates
2017-11-05 13:41:08 cri
A ranar 3 ga wata a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li keqiang ya gana da babban darektan kamfanin makamashin Terra na kasar Amurka, wanda kuma ya kafa kamfanin Microsoft wato Bill Gates.

A yayin ganawar, Firaminista Li ya bayyana cewa, bangarorin Sin da Amurka suna gudanar da hadin kai yadda ya kamata a fannin nazarin sabuwar fasahar samar da lantarki ta hanyar makamashin nukiliya, wannan wani babban ci gaba ne da suka samu a fannin. Kasar Amurka na da fasahohin zamani, kasar Sin ma na da makoma mai kyau a nan gaba, an yi imanin cewa, bangarorin biyu za su cimma moriyar juna da samun nasara tare ta hanyar hadin kai.

Firaminista Li ya nuna cewa, yanzu ana neman zurfafa kwaskwarimar sabbin sana'o'i a duniya. Kasar Sin na fatan hada albarkatun kwararru da ta samu tare da sabbin fasahohin na kasashen ketare, don kara amfana wa dan Adam.

A nasa bangaren, Bill Gates ya bayyana cewa, sabon makamashin nukiliya na da muhimmanci kwarai kan bunkasuwar fasahohin makamashi a nan gaba, kamata ya yi a bada tabbacin samar da makamashi mai tsabta da tsaro. Kamfaninsa na maida hankali sosai don yin hadin kai tare da kamfanonin kasar Sin a wannnan fannin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China