Gidan talabijin na Morocco Medi1TV ya rawaito cewa, an yiwa tauraron dan adam din lakabin "Mohammed VI-A," wanda ake saran harbawa sararin samaniya.
Za'a harba tauraron dan adam din ne a cibiyar harba tauraron dan adam ta Guiana, kuma Thales Alenia Space da Airbus sun samar da tauraron ne cikin hadin gwiwa.
A cewar kamfanin Arianespace group, tauraron dan adam din na Mohammed VI-A, za'a yi amfani dashi ne wajen gudanar da aiyukan binciken taswira da filaye, da safiyo, da bincike a fannin aikin gona, da rikakafin afkuwar bala'u, da kare muhalli, da kiyaye kwararowar Hamada, da kuma aikin tsaron kan iyakokin kasar da tekunan kasar.