in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin IOC ya bullo da takardar shawo kan matsalar cin zarafin 'yan wasa
2017-11-04 13:19:57 cri
kwamitin shirya wasannin motsa jiki na Olympics na duniya, wato IOC a takaice, ya fitar da wata sabuwar takardar bayani, a wani kokari na taimakawa hadaddiyar kungiyar wasannin motsa jiki ta duniya, da kwamitocin shirya wasannin motsa jiki na Olympics na kasashe daban-daban, wajen tsara manufofin kare 'yan wasa.

Kwamitin ya gabatar da takardar ne jiya Jumma'a, a wajen babban taron kwamitocin shirya wasannin motsa jiki na Olympics na kasashe daban-daban wanda aka yi a birnin Prague na kasar Czech.

Wannan wani muhimmin mataki ne da kwamitin IOC ya dauka, a fannin kare 'yan wasa daga lalata gami da cin zarafi.

A wajen dandalin tattaunawa tsakanin 'yan wasan motsa jiki na duniya wanda aka yi a shekara ta 2015, an yi kira da a kara daukar kwararan matakan tabbatar da tsaron 'yan wasa. Sai dai sabuwar takardar bayani da kwamitin IOC ya fitar a wannan karo, wani ci gaba ne na wancan dandalin tattaunawa, kana wani sabon bayani ne da ya shafi matakan hana lalata gami da cin zarafin 'yan wasa na kwamitin IOC.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin IOC, Thomas Bach ya bayyana cewa, ya fahimci irin damuwar da 'yan wasan motsa jiki ke nunawa, inda ya ce, tsaron 'yan wasan na da muhimmancin gaske ga kwamitin IOC gami da wasannin motsa jiki na Olympics na duniya, haka kuma kamata ya yi a tabbatar da tsaro da kare hakkinsu 'yan wasan yadda ya kamata. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China