in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Turkiyya ya lashi takobin murkushe sansanonin 'yan ta'adda dake kasashen Iraki da Siriya
2017-11-04 12:55:30 cri
Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya lashi takobin murkushe dukkanin sansanonin 'yan ta'adda dake kasashen Iraki da Siriya, inda kuma ya sake zargin wasu kasashen yammacin duniya da goyon-bayan wadannan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Yayin da yake gabatar da jawabi a jihar Manisa dake yammacin Turkiyya, Erdogan ya ce, a halin yanzu akwai sassa da dama a Iraki da Siriya wadanda ke hannun 'yan ta'adda. Ya ce, domin kare 'yan Turkiyya dake wadannan kasashe, gwamnatin kasar ta yanke shawarar murkushe ayyukan ta'addanci a kasashen ketare. Har wa yau, Erdogan ya sake zargin wasu kasashen kawayen Turkiyya dake yammacin duniya, ciki har da Amurka, da samar da tallafi da goyon-baya ga kungiyar Kurdistan Worker's Party gami da dakarun Kurdawa dake kasar Siriya.

A nasa bangaren, mai magana da yawun ma'aikatar tsaron cikin gida na Rasha, Igor Konashenkov cewa ya yi, sojojin saman Rasha gami da rundunar sojan ruwan kasar, sun kai wani gagarumin farmaki ta sama da cikin ruwa, kan mayakan kungiyar IS dake jihar Deir ez-Zor ta kasar Siriya, lamarin da ya murkushe cibiyoyin bada umurni da wuraren ajiye makamai da harsasai da dama na kungiyar, tare kuma da hallaka mayakan IS da dama. Konashenkov ya ce, wannan farmakin da sojojin Rasha suka kai, ya taimaka sosai ga matakan soji da dakarun gwamnatin Siriya suka dauka kan kungiyar IS a yankunan gabashin kasar. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China