A kwanakin baya ne, ma'aikatar kudin Amurka ta bullo da wasu sabbin matakai na kakabawa Rasha takunkumin da ya shafi sabon makamashi.
Game da wannan batu, Alexander Novak ya bayyana cewa, kamfanonin kula da sabon makamashi na Rasha na cigaba da yin nazarin matakan da za su dauka domin tinkarar takunkumin da Amurka ta sanya, tare kuma da daidaita manufofinsu na yin hadin-gwiwa da kamfanonin kasashen waje.(Murtala Zhang)