in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire ta kaddamar da babbar tashar samar da lantarki ta ruwa da kasar Sin ta gina
2017-11-03 11:01:24 cri
A jiya Alhamis kasar Cote d'Ivoire ta kaddamar da wata tashar samar da wutar lantarki ta ruwa mafi girma a kasar wanda kamfanin kasar Sin ya gudanar da aikin.

Madatsar ruwan tana da tsawon kilomita 4.5, kuma tana mafadar ruwa ta Naoua dake kogin Sassandra, kuma tana iya samar da karfin lantarki megawatts 275, ana saran zata kara karfin lantarkin da kasar Cote d'Ivoire ke samarwa ta ruwa, hakan zai baiwa kasar damar zama a sahun gaba wajen samarwa da kuma rarraba wutar lantarki a a yammacin Afrika.

Aikin na Soubre, an yi watsi dashi a shekaru da dama sakamakon rashin isassun kudaden gudanarwa, sai dai daga baya an kaddamar da shi ne a watan Fabrairun shekarar 2013 bayan da kasar Sin ta samar da kudaden gudanar da aikin.

Kamfanin samar da lantarki ta ruwa na Sinohydro wanda ke karkashin kamfanin lantarki na PowerChina, ya bayyana cewa, aikin na Soubre ya fara bada hasken lantarkin ne tun a watan Mayu, wato watanni 8 gabanin yadda aka tsara.

Gwamnatin Cote d'Ivoire ta yi matukar gamsuwa da ingancin aikin na Soubre hydroelectric dam, da kuma yadda ya gudana cikin sauri, shugaban kasar Cote d'Ivoire, Alassane Ouattara, shi ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da aikin tashar samar da lantarkin.

Ya bayyana cewa, kasar Cote d'Ivoire a shirye take ta cigaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China