in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi kira da a kawo karshen cin mutuncin 'yan jarida
2017-11-03 10:32:45 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kawo karshen laifukan cin mutuncin da musgunawa 'yan jarida, ya na mai cewa 9 daga cikin mutane 10 dake aikata laifin na kaucewa fuskantar hukunci.

A sakonsa na ranar kawo karshen cin mutuncin 'yan jarida ta duniya, Antonio Guterres ya ce daga shekarar 2006 zuwa 2016, an kashe jimilar 'yan jarida da ma'aikatan kafafen yada labarai 930, sannan dubbai na fuskantar cin zarafin da barazana da wulakanci tare da tserewa. Ya na mai cewa cin mutunci ya fi kamari cikin laifuffukan.

Ya ce cikin 'yan makonnin da suka gabata, an kashe wata fitacciyar 'yar jarida mai binccike, inda aka sanya mata bom a cikin mota a kasar Malta, kana an samu gawar wani dan jarida mai daukar hoto, bayan an sa masa bindiga tare da tilasta masa barin gidansa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China