Rahoton da aka gabatar a wajen dandalin tattauna harkokin tattalin arzikin duniya mai hedikwata a birnin Geneva na kasar Switzerland, ya ce duk da cewa an samu raguwar wariyar jinsi, karon farko a bana, daidaiton jinsi a duk fadin duniya ya samu koma-baya. Har wa yau, kasar Iceland ta sake zama kasar da ta fi tabbatar da daidaiton a duniya.(Murtala Zhang)