in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Rasha
2017-11-02 13:24:07 cri

A jiya Laraba 1 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev, inda Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Rasha kasa ce mafi girma dake makwabcin kasar Sin da ta hadin gwiwar Sin a dukkan fannoni, Sin ta tsaya tsayin daka kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da Rasha. A wannan rana, an yi ganawar dake tsakanin firaministan Sin da na Rasha karo na 22, inda firaministocin kasashen biyu suka yi musayar ra'ayoyi kan fadada hadin gwiwar kasashen biyu tare da daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa kimanin 20.

Yayin da ake cika mako daya bayan gama babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS karo na 19, firaministan kasar Rasha Dmitry Medvedev ya kai ziyara a kasar Sin, wanda ya zama jagoran gwamnatin kasar waje na farko da ya kai ziyara a kasar Sin bayan gama babban taron wakilan JKS karo na 19. Ba da dadewa ba, shugaban kasar Amurka Donald Trump zai kai ziyara a kasar Sin bisa gayyatar da aka yi masa, ziyarar Medvedev ta bude sabon jerin ziyarar manyan shugabannin kasashen waje a kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi maraba da Medvedev ya kai ziyara a kasar Sin bayan babban taron wakilan JKS karo na 19, Xi Jinping ya bayyana cewa,  

"A ganina, wannan wata dama ce, kasar Sin tana shiga sabon lokaci, mu tattauna yadda za a sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha. Sin ta tsaya tsayin daka kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da Rasha, tana son yin kokari tare da Rasha wajen fadada hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, da neman makoma iri bai daya ta dan Adam."

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kamata ya yi Sin da Rasha sun yi amfani da tsarin ganawar dake tsakanin firaministocin kasashen biyu wajen inganta hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin makamashi, kere-kere, aikin gona, nazarin sararin samaniya da sauransu, da ci gaba da yin kokarin yin kirkire-kirkire yayin da ake raya hadin gwiwarsu, da maida fannin sadarwa na zamani a matsayin sabon fannin bunkasa hadin gwiwarsu.

Medvedev ya ce, kasar Rasha tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin a dukkan fannoni, da yin mu'amala da juna kan harkokin kasa da kasa da na yankuna.

A wannan rana, firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaran aikinsa na Rasha Medvedev sun yi ganawar dake tsakanin firaministocin kasashen biyu karo na 22, tare da bayar da hadaddiyar sanarwa, kana an daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa kimanin 20 dake shafar fannonin zuba jari, makamashi, hadin gwiwar dake tsakanin yankuna, al'adu, aikin gona da sauransu.

Yayin da suke ganawa da 'yan jarida tare, Li Keqiang ya bayyana cewa, bangarorin biyu suna son yin kokari tare don inganta hadin gwiwarsu a fannin tattalin arziki da cinikayya yadda ya kamata. Li Keqiang ya bayyana cewa,

"Mun yabawa dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha a fannin tattalin arziki da cinikayya. Tun daga bana, cinikin dake tsakanin kasashen biyu ya karu sosai, bangarorin biyu sun tattauna da zurfafa da fadada cinikinsu, da aiwatar da ayyukan da aka cimma, da kara neman sabbin fannoni na hadin gwiwarsu."

A ganawar a wannan karo, bangarorin biyu sun tattauna ci gaba da yin hadin gwiwa a fannonin man fetur da iskar gas, da aiwatar da ayyukan hadin gwiwarsu da yarjejeniyoyin da gwamnatocin kasashen biyu suka daddale, da kara yin hadin gwiwa a fannin samar da wutar lantarki, da makamashin da za a iya sake yin amfani da shi da sauransu. Medvedev ya bayyana cewa,

"Na taya murnar gudanar da babban taron wakilian jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19 cikin narasa, wanda yana da babbar ma'ana ga kasar Sin har ma ga dukkan duniya gaba daya. Yanzu ana raya dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin mai kyau, tun daga bara zuwa watan Yuni na bana, yawan cinikin dake tsakanin kasashen biyu ya karu da kashi 35 cikin dari, kana zai ci gaba da karuwa a fannoni daban daban ciki har da masana'antu da nazarin sararin samaniya."

Medvedev ya kara cewa, kasar Rasha tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin makamashi, ayyukan more rayuwa, samar da kayayyaki, ciniki ta internet, matsakaici da kananan kamfanoni, al'adu da sauransu, ta haka za a sa kaimi ga inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China