in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Mugabe na Zimbabwe ya amince da zartar da hukuncin kisa a kasarsa
2017-11-02 10:28:55 cri

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya sanar da aniyarsa ta amincewa da a zartar da hukuncin kisa a kasarsa sakamakon yawaitar kashe rayukan da ake samu.

Shugaban ya nuna damuwa kan karuwar laifukan fyade da kisan gilla a kasar Zimbabwe, inda ya bukaci 'yan kasar da su mutunta rayukan bil adama.

Kiran na mista Mugabe, ya zo ne bayan hallaka wata 'yar uwar jagoran cocin Roman Catholic na kasar Ruvadiki Plaxedes Kamundiya, wanda ya faru kwanan nan a Mutoko, Mashonaland lardin gabashin kasar.

Ana tsare da wani mutum bisa zarginsa da laifin yiwa matar fyade, daga bisani kuma ya kashe ta, ya kuma jefa gawarta a cikin wani kududdufi dake kusa da yankin.

Mugabe, ya bukaci a zartar da hukunci mafi girma kan wannan laifin.

Dokar kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe ta shekarar 2013, ta amince a zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wani mutum namji daga dan shekara 18 zuwa 70 da aka samu laifin aikata kisan kai, sai dai mata da kananan yara, an tsame su daga cikin wannan hukunci.

To sai dai kuma, gwamnatin Zimbabwen ba ta taba aiwatar da wannan hukunci ba tun a shekarar 2005 saboda rashn tanadar wanda zai aiwatar da hukuncin ratayar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China