in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ganawa tsakanin shugabannin Sin da Amurka za ta tsara manufar raya hulda tsakanin kasashen biyu
2017-11-01 10:57:00 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai kawo ziyara nan kasar Sin daga ranar 8 zuwa 10 ga wannan wata, a gabannin ziyarar, jakadan kasar Sin dake wakilci a Amurka Cui Tiankai, ya zanta da manema labaran kafofin watsa labaran kasar Sin da sauran kasashen duniya, a ofishin jakadancin kasar Sin dake Amurka a ranar 30 ga watan Oktoban da ya gabata, inda ya bayyana cewa, babban makasudin ziyarar da Trump zai kai a kasar Sin shi ne tsara sabuwar manufar raya huldar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba, tare kuma da kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

Shugaban Amurka Trump ya zama shugaban kasa na farko wanda zai kai ziyara a kasar Sin, tun bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi cudanya da shi a cikin watanni da dama da suka gabata; misali shugabannin biyu sun taba ganawa da juna sau biyu, kuma sun taba tattaunawa ta waya sau 8, kana sun taba aikewa juna sakwanni sau da dama. Jakada Cui Tiankai ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan ziyarar aikin da shugaba Trump zai kai a kasa, ya ce, "Shugaba Trump zai yi ziyarar aiki ta farko a kasar Sin, muna mai da hankali matuka kan ziyarar, kuma mun shirya wasu ayyukan share fage na musamman domin hakan, da ma iyalinsa baki daya. Dalilin hakan shi ne domin tabbatar da cewa, shugabannin kasashen biyu sun samu damar tattaunawa yadda suke fata yayin ziyarar, ganin cewa lamarin yana da muhimmincin gaske ga huldar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Amurka."

Tattaunawar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu za ta daidaita rashin fahimtar dake tsakanin sassan biyu, kuma za ta shawo kan sabanin dake tsakaninsu. Ban da haka kuma za ta sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, tare kuma da tsara sabuwar manufar raya huldar dake tsakaninsu. Har wa yau kasashen duniya da dama suna sa ran cewa, kasashen Sin da Amurka za su kafa huldar abokantaka tsakaninsu.

Jakada Cui Tiankai ya ci gaba da cewa, an kimmanta cewa, shugabannin biyu za su yi tattaunawa kan wasu abubuwan da suka fi jawo hankalinsu; misali batun nukiliya a zirin Koriya, da batun tattalin arziki da ciniki dake tsakanin Sin da Amurka da sauransu. Game da batun nukiliya a zirin Koriya, Cui Tiankai ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin ta yi kokari matuka domin daidaita batun lami lafiya, kuma kasar Sin tana aiwatar da kudurin kwamitin tsaron MDD yadda ya kamata, har ta rasa babbar moriyarta, shi ya sa tana fatan sauran kasashen duniya za su iyar nuna mata goyon baya, ya ce, "A sa'i daya kuma, ba zai yiwu ba kasar Sin ita kadai ta warware batun nukiliyar zirin Koriya, dole ne sai sassan da abun ya shafa kamar su Amurka da Koriya ta Arewa sun yi kokari tare. A bayyane take cewa idan har kasar Sin ita kadai ke wannan kokari, ba zai yiwu a kai ga warware batun na zirin Koriya ba, kuma hakan zai sa yanayin da yankin ke ciki ya kara tsanani, a karshe ya kai ga haifar da illa ga moriyar sassa daban daban."

Game da makomar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da ciniki, Cui Tiankai ya bayyana cewa, sassan biyu sun fi mai da hankali kan cinikin dake tsakaninsu bisa tushen adalci da moriyar juna, inda ya ce, "Tun daga shekara mai zuwa, za mu shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su daga kasashen ketare a birnin Shanghai dake kudancin kasar Sin, wannan sabon mataki ne da kasar Sin za ta dauka, domin sa kaimi ga harkar shigo da kayayyaki daga kasashen ketare. Ko shakka babu, hakan zai samar da dama ga kamfanonin kasar Amurka, wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin. A shirye muke mu kara sayen kayayyakin da muke bukata daga kasashen ketare."

Jakada Cui Tiankai ya kara da cewa, yana fatan abokan Amurka za su karanta rahoton da aka fitar bayan da aka kammala babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, saboda daga rahoton, za su iya gano cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje, a saboda haka 'yan kasuwan Amurka za su kara samun damammakin gudanar da ciniki a kasar Sin, yana kuma fatan za su yi amfani wadannan damammaki, ta yadda za a raya huldar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata.

Kaza lika, jakada Cui Tiankai ya amsa wasu tambayoyin da manema labarai suka yi masa game da batun kudancin teku, da batun Taiwan, da makomar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka kan shawarar "Ziri daya da hanya daya" da sauransu, inda ya bayyana cewa, ba ma kawai babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19 ya tsara manufar raya kasar Sin ba, har ma ya samar da damammakin da ba a taba ganin irinsu ba a tarihi ga kasar Sin, domin ta raya huldar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, ciki har da kasar ta Amurka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China