in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta alkawarta ci gaba da tallafawa al'ummar Syria
2017-10-31 10:40:01 cri
Jakadan Sin a kasar Syria ko Sham Qi Qianjin, ya bayyana kudurin kasar sa, na ci gaba da baiwa kasar ta Syria da yaki ya daidaita tallafi, domin saukakawa al'ummar ta radadin matsi da suke fuskanta.

Qi Qianjin ya bayyana hakan ne, yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai wasu sassan kasar dake birnin Manin na arewa da Damascus, inda aka yi amfani da tallafin kasar ta Sin wajen samar da gidan burodi, da kayan kiwon lafiya, da wurin dafa abincin ga mabukata.

Kasar ta Sin ta samar da wannan tallafi ne karkashin inuwar kungiyar Red Cross da hadin gwiwar takwarar ta ta Syria wato SARC.

Da yake karin haske game da hakan, Mr. Qi ya ce a watan Mayu, gwamnatin kasar Sin ta samar da tallafin kudi har dalar Amurka miliyan 1 ga Red Cross, don gudanar da ayyukan jin kai a Syria, ayyukan da suka hada da samar da tsaftacaccen ruwan sha, da abinci, da wuraren kwana na wucin gadi, da kayan kiwon lafiya ga wandanda tashe tashen hankula suka raba da muhallan su a cikin kasar da wadanda ke kasashe makwafta.

Jami'in ya ce Sin na hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya WHO, da shirin abinci na duniya WFP, wajen gudanar da ayyuka daban daban a Syria, tana kuma fatan hakan zai rage radadin wahalhalu da al'ummar Syria ke fuskanta, tare da karfafa matakan siyasa da ake da su, a wani mataki na warware turkaturkar siyasar kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China