Liu Lu, shugaban kungiyar masana cutukan zuciya na kasar Sin ya bayyana cewa, likitocin daga kasashen Indonesia da Mauritius sun samu horo a wasu asibitoci daga biranen Beijing da Shanghai.
A shekarar data gabata ne hukumomin lafiya na kasar Sin suka amince da shirin bada horon domin inganta fasahar likitocin kasashen dake kan hanyar ziri daya hanya daya.
Kwasa-kwasan sun fara ne daga mako guda zuwa watanni 3. Sai kuma wanda ya yafa daga watanni 6 zuwa shekara guda.
Ana sa ran wasu karin kasashen dake kan hanyar ziri daya da hanya daya za su amfana da shirin.
Bayan cigaban da ta samu shekaru 30 a fannin bada tallafi game da cutukan zuciya, kasar Sin ta samu babban matsayi na yin gogayya a matakin kasa da kasa a fannin kimiyyar cutukan zuciya.(Ahmad Fagam)