in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta nanata aniyarta na hadin gwiwa da Amurka
2017-10-30 11:49:26 cri
Gwamnatin Sudan ta jaddada aniyarta na inganta hadin gwiwa da kuma kyautata mu'amala da kasar Amurka.

Sakataren ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan Abdul-Ghani Al-Naeem, ya bayyana hakan a lokacin wata tattaunawa a birnin Khartoum da mataimakin sakataren kula da harkokin kudi da takunkumi na hukumar kula da tattalin arziki da kasuwanci na kasar Amurka wanda ke ziyarar aiki a Sudan.

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Sudan din ta fitar, sakataren ya jaddada aniyar Sudan na cigaba da karfafa kyakykyawar dangantaka da hadin gwiwa da kasar Amurka a dukkan matakai.

Ya kuma nanata aniyar kasar Sudan wajen gina kyakkyawar dangantaka wacce zata tabbatar da zaman lafiya da kuma cigaban kasashen biyu.

A ranar 6 ga watan Oktoba ne, Amurka ta yanke shawarar dage takunkumin tattalin arziki na dindindin ga kasar Sudan, inda ta bayyana irin cigaban da Sudan din ta samu game da matakan data dauka na magance tashe tashen hankula a yankunan da ake fama da rikici a kasar, da bada damar shigar da kayan agaji ga yankunan, da kuma tabbatar da hadin gwiwa da Amurka don yin aiki tare wajen shawo kan matsalolin tashin hankali da magance barazanar ta'addanci a sassan kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta bada sanarwa cewa, matakin data dauka na janye takunkumin zai fara aiki ne daga ranar 12 ga watan Oktoba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China