in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barzani ya sauka daga mukamin shugaban yankin Kurdawa
2017-10-30 10:04:10 cri

Shugaban yankin Kurdawa mai kwarya kwaryar 'yanci a Iraqi Masoud Barzani, ya bayyanawa wani taron 'yan majalissar yankin da ya gudana a jiya Lahadi aniyar sa, ta sauka daga mukamin sa tun daga ranar 1 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Mr. Barzani ya bayyanawa taron 'yan majalissar hakan ne a birnin Erbil, fadar yankin na Kurdustan. Ya ce, sauya dokar jagoranci ko tsawaita wa'adin mulkin shugaba a yankin, ba abu ne da ya dace a lamunta ba.

Daga nan sai ya yi kira da a gaggauta gudanar da taro, ta yadda za a kaucewa haifar da gibi na aiki a ofishin jagoran yankin.

Barzani ya kuma bukaci 'yan majalissar dokokin da su rarraba ikon jagorancin yankin a fannin dokoki da tsaro, da na gudanarwa, ga tsagin zartaswar yankin, da na 'yan majalissa da na shari'a.

Duk dai da cewa ya yi sallama da mukamin na sa, Barzani ya alkawarta ci gaba da sadaukar da kai wajen fafutukar ganin al'ummar yankin ta samu ci gaba da wadata, tare da kare irin nasarori da aka riga aka cimma.

Bayan da Mr. Barzani ya gabatar da wasikar ajiye aiki, 'yan majalissar dokokin yankin sun ci gaba da zaman su, inda suka amince da zabar firaministan yankin Nechirvan Barzani, a matsayin babban kwamandan askarawan yankin na Kurdistan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China