in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 28 sun mutu sanadiyyar hadarin mota a yammacin Nijer
2017-10-28 13:21:36 cri

An samu wani mumman hadarin mota a birnin Dosso da ke yammacin kasar Nijer da safiyar jiya Jumma'a, inda mutane a kalla 28 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 24 suka jikkata.

Kafofin yada labaru na Nijer, sun ruwaito hukumar kula da harkokin sufuri ta kasar na cewa, wata motar kasuwa ta yi taho mu gama da wasu kananan motoci biyu a kan titin birnin Dosso da misalin karfe 6 na safiyar jiya, inda mutane a kalla 28 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 24 suka jikkata. Yanzu haka dai wadanda suka jikkatan na asibitin da ke kusa da inda hadarin ya abku.

Sakamakon binciken farko da hukumar kula da harkokin sufuri ta kasar ta gabatar ya shaida cewa, motar kasuwar mai cike da fansinjoji na gudun wuce sa'a, a lokacin da ta koma daya hannun titin yayin da take yunkurin wuce wata mota, al'amarin da ya janyo mata cin karo da wasu motoci biyu da suka fito daga Nijeriya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China