in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya nemi goyon baya game da yadda za'a sake gina CAR
2017-10-27 09:45:27 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci taimakon kasa da kasa domin sake gina jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, bayan da rikici ya daidaita kasar.

A rana ta uku ta ziyarar aikin da yake yi a CAR, mista Guterres ya ce ya zama tilas a samar da kudaden da za'a yi amfani da su wajen sake gina kasar domin inganta rayuwar jama'ar kasar, kana dole ne gwamnatin kasar ta gudanar da ayyukan da za su tabbatar da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma cigaban kasar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Bangui babban birnin kasar, Guterres ya ayyana wasu batutuwa hudu a matsayin wasu ginshikan da za'a mayar da hankali kansu, wadanda suka hada da tsaro, sake gina kasa, hada kan kasa, da kuma samar da cigaba, wanda a cewarsa hakan ne zai kara tabbatar da gina dauwamammen zaman lafiya da farfado da cigaban kasar.

Game da sha'anin tsaro kuwa, Guterres ya ce an bukaci kwamitin tsaron MDDr ya kara yawan jami'ansa dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, kuma a samar musu da isassun kayan aiki domin su kare rayukan fararen hula a CAR.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China