in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: Ya dace Afirka ta fadada ribar da take samu daga albarkatu ta hanyar inganta darajar su
2017-10-26 20:14:59 cri

Ministan ma'aikatar kudi na kasar Zimbabwe Ignatius Chombo, ya ce kamata ya yi kasashen dake nahiyar Afirka, su dauki matakan fadada ribar da suke samu daga hajojin da ake fitarwa wajen nahiyar, ta hanyar kara musu daraja don kaucewa saukar farashi.

Mr. Chombo ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, a jawabin sa na bude taro karo na 23, na kwamitin kwararru game da raya kudancin Afirka, wanda aka gudanar a birnin Bulawayo.

Ministan ya kara da cewa, kamata ya yi kasashen nahiyar Afirka su bunkasa harkokin cinikayyar su, ta hanyar magance matsaloli masu nasaba da karancin ababen more rayuwa, da kuma dokokin dake shafar kan iyakokin su.

Ya ce duk da cewa bunkasar tattalin arziki a kasashe masu saurin ci gaba, wato Sin da India, da Brazil da Rasha, na da tasiri kan irin hajojin da ake fitarwa daga nahiyar Afirka, a hannu guda akwai bukatar fadada hanyoyin cimma riba a nahiyar, ta yadda hakan zai taimaka ga samun nasara mai dorewa.

Taron na wannan karo dai na da taken "Bunkasa cinikayya a kudancin nahiyar Afirka: da rage gibin ababen more rayuwa".(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China