Wani jami'in tsaro ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ta wayar tarho cewa, lamarin ya faru ne a wani yanki tsakanin Arbiska da Lafole a kusa da garin Afgoye, dake da tazarar kilomita 30 daga Mogadishu babban birnin kasar.
Mai Magana da yawun dakarun na AMISOM Wilson Rono, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kashe mutanen ne a lokacin fafatawa tsakanin dakarun AU da mayakan Al-Shabaab.
Rono yace AMISOM ta yi hasarar sojinta guda kuma wani sojin guda ya samu raunuka.
Amma wata majiya mai zaman kanta ta ambato cewa, a kalla sojojin AU 3, da wasu malamai 2, da dalibai, da masu gadi da kuma mayakan Al-Shabaab 4 ne aka kashe a lokacin arangamar.(Ahmad Fagam)