in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa dake amfani da Intanet na da tabbacin tsaron yanar gizo
2017-10-24 10:50:20 cri
Wani bincike da wani kamfanin tsaron intanet na kasar Sin ya fitar ya nuna cewa, kimanin kaso 90 cikin 100 na Sinawa dake amfani da Intanet na da tabbaci game da yadda mahukuntan kasar ta Sin ke daukar matakan tsaro kan yanar gizo. Ko da yake rahoton ya ce, kaso 19 cikin 100 na al'ummar Sinawa ba su da masaniya game kutse na baya-bayan kan shafukan intanet.

Rahoton ya kara da cewa, kimanin kaso 56 cikin 100 na Sinawan dake amfani da yanar gizo, sun nuna gamsuwa da yanayin Intanet na kasar, yayin da kimanin kaso 32.8 cikin 100 na masu amfani da yanar gizo ke cewa, akwai kyakkyawan yanayin tsaron Intanet.

A hannu guda kuma, kimanin kaso 40 cikin 100 na masu amfani da wannan kafa na cewa, za su mayar da hankali sosai kan manyan kutse na baya-bayan da aka kai kan shafukan gizo, kamar kutsen baya-bayan na WannaCry, yayin da sama da kaso 26 cikin 100 na masu amfani da Intanet ke cewa, irin wadannan kutse ba za su shafi harkokinsu na rayuwa ba.

Yanzu haka dai, kimanin kaso 90 cikin 100 na masu amfani da yanar gizo a nan kasar sun sanya manhajojin kariya daga tsutsar kwanfuta a wayoyinsu na salula da kwanfutocinsu.

A cewar cibiyar kula da harkokin Intanet ta kasar Sin, ya zuwa watan Yulin wannan shekara yawan masu amfani da yanar gizo a kasar Sin ya kai mutane miliyan 751, karuwar kaso 2.7 cikin 100 ya zuwa karshen shekarar 2016. Yanzu haka akwai Sinawa miliyan 724 da ke amfani da wayoyinsu na salula wajen shiga yanar gizo, adadin da ya kai kaso 96.3 cikin 100 na yawan masu amfani da yanar gizo a kasar. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China