in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zaben Iraqi ta ayyana 12 ga Mayu a matsayin ranar babban zaben kasar
2017-10-23 12:12:44 cri

Hukumar zaben kasar Iraqi ta tsayar da ranar 12 ga watan Mayun shekarar 2018 a matsayin ranar zaben majalisar dokokin kasar wadda za ta shafe wa'adin shekaru 4.

Mataimakin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar IHEC, Gatie al-Zouba'i, ya fada cikin wata sanarwa cewa, majalisar kwamishinonin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (IHEC) ne suka amince da ranar taron majalisar gudanarwar firaiministan kasar Haider al-Abadi, a matsayin sabuwar ranar gudanar da zaben majalisar dokokin kasar wanda za ta shafe wa'adin shekaru hudu.

Bisa ga dokokin kundin tsarin mulkin kasar Iraqi, wajibi ne a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a kalla kwanaki 45 gabanin karewar wa'adin majalisar dokokin mai ci a halin yanzu, kuma dole ne majalisar gudanar da mulki ta Abadi ta shirya zaben tare da hadin gwiwar IHEC. Kuma wajibi ne majalisar dokokin ta yanzu ta amince da matakin daga bisani kuma ta turawa majalisar koli ta kasar domin samun cikakkiyar amincewarta.

A ranar 30 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne aka gudanar da babban zaben kasar Iraqi, a lokacin ne 'yan kasar suka zabi mambobin majalisar 328, wadanda su ne suka zabi Abadi don samar da gwamnatin hadaka da ta hada da Shi'a Kurds da Sunnis.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China