in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saudiya da Iraki za su kafa hukumar hadin gwiwa
2017-10-23 11:12:35 cri

A jiya Lahadi ne a birnin Riyadh kasashen Saudiya da Iraki suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kafa hukumar hadin gwiwa, wadda ake fatan za ta bude wani sabon babi na inganta alaka tsakanin kasashen biyu wadanda suka shafe sama da shekaru 20 ba sa dasawa.

Manufar kafa wannan hukuma wadda majalisar zartarwar masarautar Saudiyar ta amince da ita a cikin watan Agustan wannan shekara, ita ce daga matsayin dangankar sassan biyu, a fannonin zuba jari da alakar al'adu, da baiwa kasar Iraki wata sabuwar kafa ta farfado da tattalin arzikinta. Yayin da Saudiya a nata bangare za ta yi amfani da hukumar da sauran matakai wajen rage karfin da Iran take da shi a kasar Iraki.

Sarkin Salman bin Abdulaziz na Saudiya da firaminista Haider al-Abadi na Iraki ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a madadin kasashen nasu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China