in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al Sisi ya bukaci jami'an tsaro da su zakulo maharan da suka halaka 'yan sanda a lardin Giza
2017-10-23 10:22:42 cri

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar ya yi kira ga hukumomin tsaron kasar da su zakulo wadanda suka kaddamar da harin ta'addancin ranar Jumma'a wanda ya yi sanadin rayukan 'yan sanda 16 a lardin Giza.

Shugaba al Sisi ya yi wannan kiran ne yayin wata ganawa da ministan tsaron kasar Sedqi Sobhi, da takwaransa na harkokin cikin gida Magdy Abdel Ghaffar, da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar Khaled Fawzi.

Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasar ta Masar Alaa Youssef ya rabawa manema labarai, ta bayyana cewa, shugaba Sisi ya kuma yi kira da a kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar don hana 'yan ta'adda shigowa cikin kasar. Ya kuma nanata kudurin kasarsa na ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci, da wadanda ke daukar nauyinsu.

Bugu da kari, shugaban na Masar ya nanata cewa, sadaukar da rayukan da 'yan sanda da aka kashe suka yi ba zai tafi a banza ba.

A ranar Asabar din da ta gabata ce, ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar ta sanar da kashe 'yan sandan kasar 16, kana ba a ji duriyar guda ba tun lokacin da suka yi musayar wuta da 'yan ta'adda ranar Jumma'a a yankin Wahat na lardin Giza dake kusa da Alkahira, babbar birnin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China