in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin AU ya bukaci jama'ar Somali su hada kai wajen yakar ayyukan ta'addanci
2017-10-22 12:38:11 cri

Babban wakilin kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya, ya bukaci al'ummar kasar da su hada kai wajen yakar ayyukan ta'addanci wanda ya haddasa hasarar rayukan al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba musamman a 'yan kwanakin da suka gabata.

Francisco Madeira, wakilin musamman na shugaban kungiyar AU, ya bukaci al'ummar Somali da su yi aiki kafada da kafada tare da jami'an tsaro domin yin galaba kan kungiyar Al-Shabaab da sauran kungiyoyin ta'addanci.

Jami'in ya yi wannan kiran ne a lokacin da manyan jami'an AMISOM da na MDD suka yi hadin gwiwa wajen jajantawa gwamnatin Somali dangane da harin bam da aka kaddamar a ranar 14 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadiyyar rayuka masu yawa.

A sanarwar da aka fitar, Madeira ya nanata cewa, wadanda suka kaddamar da harin da ya haddasa rayukan fararen hula suna rayuwa ne a cikin al'umma, don haka ya bukaci al'ummar da su baiwa jami'an tsaro muhimman bayanan da za su taimaka wajen zakulo wadanda suka aikata laifukan.

A kalla mutane 358 ne aka kashe a lokacin harin wanda aka yi amfani da wasu motoci da aka makare su da abubuwan fashewa, inda aka girke su a wajen dake da yawan cunkoson jama'a a kusa da birnin Mogadishu.

Shugaban tawagar jami'an MDD dake aiki a Somali (UNSOS), Hubert Price, ya yi Allah wadai da kaddamar da harin, kana ya nanata bada goyon bayan MDD don tallafawa kasar Somalia.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China