in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe 8 masu tasowa na tattauna hanyoyin bunkasa cinikayya
2017-10-20 10:32:08 cri

Manyan jami'an kungiyar kasashe 8 masu tasowa, sun hadu a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a jiya Alhamis, domin tattauna hanyoyin bunkasa huldar cinikayya a bangarori daban-daban, domin tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta.

Yayin bude taron, ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu, ya ce akwai bukatar kasashen su yi amfani da arzikinsu yadda ya kamata, ta hanyar samar da hadin gwiwa a wasu bangarori da dama.

Mevlut Cavusoglu, ya jadadda cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashen kungiyar da suka hada da Bangladesh da Masar da Indonesia da Iran da Malaysia da Nijeriya da Pakistan da Turkiyya, abu ne mai matukar muhimmanci, a daidai lokacin da suke fuskantar kalubalen da suka hada da wariyar launin fata da talauci da 'yan gudun hijira da fari.

Ya ce, kasashen dake wakiltar kimanin kaso 15 bisa dari na al'ummun duniya na da dimbin damammaki da ma'adinai da yawan jama'a.

Ya yi kira da su inganta hadin giwa a bangaren makamashi domin bunkasa kasashen, tare da inganta huldar kasuwanci tsakaninsu a fannonin aikin gona da masana'antu da muhalli da yada labarai da sufuri, domin tunkar kalubalen.

Kungiyar ta kasashe 8 da aka kafa a shekarar 1997, kungiya ce dake da nufin inganta hadin gwiwa tsakanin mambobinta.

An shirya gudanar da taro a yau Juma'a domin bikin cikar kungiyar shekaru 20 da kafuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China