in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin ruwan Sin na Peace Ark ya isa Angola don samar da taimakon kiwon lafiya
2017-10-20 09:31:02 cri

Jirgin ruwan kasar Sin mai dauke da cibiyar kiwon lafiya wato Peace Ark ya isa Luanda, babban birnin kasar Angola da safiyar ranar Alhamis don gudanar da aikin kula da lafiyar jama'a kyauta na tsawon kwanaki 8 a kasar.

Guan Bailin, shi ne kwamandan tawagar jami'an kula da lafiyar, ya bayyana cewa, wannan shi ne karon farko da Peace Ark ya ziyarci Angola, kuma manufar wannan shirin ita ce domin karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu.

Mista Guan ya ce, a shekarar 2008 ne aka kaddamar da shirin aiki da Peace Ark, kuma kawo yanzu shirin ya ziyarci kasashe 34, domin gudanar da tallafin aikin jinya kyauta.

Tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015, Peace Ark ya ziyarci nahiyoyin Asiya, Afrika, da Amurka da Oceania. Kimanin mutane 120,000 daga kasashe 29 da sassa daban-daban na duniya ne suka amfana da shirin kula da lafiya kyauta da kuma aikin jin kai ga al'ummomin kasa da kasa.

Da zarar Peace Ark ya kammala aikinsa a kasar Angola, zai ziyarci kasashen Mozambique da Tanzania da sauran kasashen duniya don gudanar da aikin kula da lafiyar da kuma aikin jin kan al'umma.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China