in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi babban taro karo na 137 na majalisun dokokin kasa da kasa a Rasha
2017-10-19 12:55:24 cri

An yi babban taro karo na 137 na majalisun dokokin kasa da kasa a birnin St.Petersburg na kasar Rasha daga ranar 14 zuwa ranar 18 ga wata, wanda ya samu halartar tawagar kasar Sin a karkashin jagorancin Zhang Ping, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin.

Babban taken taron shi ne "tattaunawa a tsakanin masu bin addinai daban daban da 'yan kabilu daban daban don kasancewar al'adu iri daban daban da zaman lafiya". A cikin jawabin da ya gabatar, Zhang Ping, ya bayyana cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ra'ayin raya makomar bil Adama bai daya, a ciki, yin cudanyar al'adu da koyi da juna wani muhimmin kashi ne. Kasar Sin na son yin kokari kafada da kafada tare da kasa da kasa don ci gaban wayewar kan dan Adam da al'adun duniya iri daban daban, ta yadda za su sa kaimi ga bunkasuwar bil Adama mai dorewa.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China