in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Nijeriya ta tura jiragen ruwan yaki da dakaru domin atisaye na musamman
2017-10-18 09:45:21 cri

Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta ce, ta tura jiragen ruwan yaki 4 da kwale-kwale masu bindiga da dakaru domin wani atisaye na musamman.

Kwamandan dakarun Rear Adm. Victor Adedipe, ya ce manufar atisayen na yini biyu da aka yi wa taken 'Exercise Pouncer' ita ce, kara horar da dakarun da suke bukata na zama cikin shiri domin magance fashin teku da sauran laifuffuka da ake aikatawa a yankunan ruwan kasar.

Victor Adedipe ya ce, atisayen sai kara karfafa kwarewar dakarun kan harkokin da suka shafi tsaron teku da dabarun shirin tunkarar aiki ba tare

Ya ce, burin rundunar shi ne kawo karshen laifuffukan da ake aikatawa a ruwa kamar fashi da satar jiragen ruwa da danyen man fetur.

Kwamnadan ya kara da cewa, za a gudanar da atisayen ne a yankunan ruwan kasar, yana mai cewa, ba zai kai gabar ruwan Guinea ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China