in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta zabi mambobi 15 na hukumarta ta kare hakkin dan Adam
2017-10-17 09:58:40 cri

Babban zauren MDD ya zabi kasashe 15 da za su kasance mambobin hukumar kare hakkin dan Adam ta majalisar.

A kuri'ar da aka kada jiya Litinin, an zabi kasashen Afghanistan da Angola da Australia da Chile da jamhuriyar demokradiyyar Congo da Mexico da Nepal da Nijeriya da Pakistan da Peru da Qatar da Senegal da Slovakia da Spaniya da kuma Ukraine, inda za su yi wa'adin shekaru 3, wanda zai fara daga 1 ga watan Junairun badi.

Daga cikin kasashe masu barin gado akwai Albania da Bangaladesh da Bolivia da Botswana da jamhuriyar Congo da El Salvador da Ghana da India da Indonesia da Latvia da Netherlands da Nijeriya da Paraguay da Portugal da kuma Qatar.

Za a iya kara zabar kasashe 11 daga cikinsu in ban da Botswana da jamhuriyar Congo da India da Indonesia.

Kasashen Nijeria da Qatar sun nemi a sake zabar su, inda kuma bukatar tasu ta samu karbuwa.

Hukumar kare hakkin dan Adam ta duniya, hukuma ce da ta kunshi kasashe daban-daban, wadda ke da nauyin ingantawa tare da kare hakkin dan Adam a duniya. Ana zabar mambobin hukumar 47 ne ta hanyar kada kuri'a cikin sirri. Inda ake bukatar rinjayen kuri'u 97 kafin samun nasara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China