in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO tana tallafawa shirin rigakafin zazzabin shawara a Najeriya
2017-10-17 09:37:09 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO tana ba da tallafin alluran rigakafin zazzabin shawara a Najeriya, inda ake sa ran yiwa mutane sama da dubu 874.

Gwamnatin Najeriyar ce ta kaddamar da aikin rigakafin na tsawon kwanaki 10 daga ranar Juma'a, inda ake sa ran yiwa mutane kimanin 873,837 allurar riga-kafin cutar a jahohin Kwara da Kogi dake yammaci da tsakiyar Najeriyar. An taba samun barkewar zazzabin shawarar a Najeriya a shekarar 2002, inda ta kama mutane 20, kuma mutane 11 da cutar ta hallaka a wancan lokaci.

Sama da jami'an kiwon lafiya 200 da kuma ma'aikatan sa kai ne za su gudanar da aikin rigakafin, inda ake sa ran yiwa mutane tsakanin 'yan watanni 9 zuwa shekaru 45. Hukumar WHO tana aiki tare da hukumomin yankunan da abin ya shafa domin samun nasarar aiwatar da shirin.

Wakilin WHO a Najeriya Dr. Wondimagegnehu Alemu ya ce, makasudin gudanar rigakafin shi ne domin tabbatar da ba da kariya ga mutanen dake zaune a yankunan dake da fargaba barkewar cutar, da kuma hana bazuwar cutar zuwa sassan kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China