in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ba da tallafin kayayyakin kiwon lafiya ga Madagascar don yaki da annobar cuta
2017-10-13 09:15:10 cri

Kasar Sin ta mika kayyayakin kiwon lafiya ga tsibirin Madagascar domin yaki da annobar cuta da ta barke cikin watanni uku da suka gabata, inda ta yi sanadin mutuwar mutane 57.

Da yake jawabi yayin mika magungunan, jakadar kasar Sin a Madagascar Yang Xiaorong, ta ce kayayyakin da darajarsu ta kai dala 220,000, kyauta ce daga gwamnati da al'ummar kasar Sin zuwa ga gwamnati da al'ummar Madagascar.

Yang Xiaorang ta ce, za a iya amfani nan take, da kayayyakin da suka hada da na aiki da magungunan yaki da cututtuka da tufafi da makarin fuska da safar hannu.

Jakadar ta kuma yi alkawarin cewa, a shirye ofishin jakadancin Sin da likitoci Sinawa suke su yi aiki da ma'aikatar kula da lafiyar al'umma da jami'an lafiya a kasar wajen yaki da cutar mai yaduwa, tare da ci gaba da fadadda hadin gwiwarsu ta fuskar kiwon lafiya.

Ta ce, a yanzu haka, akwai likitoci Sinawa 30 dake aiki da takwarorinsu na Madagascar a asibitoci 4, domin kula da wadanda suka kamu da cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China