in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Qatar: An ki amincewa da yin shawarwari kan ikon daukar bakuncin gudanar da gasar cin kofin duniya
2017-10-12 11:03:40 cri
Shugaban ofishin watsa labaru na gwamnatin kasar Qatar Sheikh Saif Bin Ahmed Al Thani, ya bayar da sanarwa a jiya ranar 11 ga wata cewa, an ki amincewa da yin shawarwari kan ikon daukar bakuncin gudanar da gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa ta shekarar 2022 da za a yi a kasar Qatar.

Game da batun kasashen da suka yanke huldar diplomasiyya da Qatar sun bukaci kasar Qatar da ta yi watsi da ikon daukar bakuncin gudanar da gasar cin kofin duniya, Saif ya bayyana a cikin sanarwar cewa, kasar Qatar za ta zama kasa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya wadda ta gudanar da gasar cin kofin duniya bisa dukkan ma'auni.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, wani jami'in bangaren 'yan sanda na kasar hadaddiyar daular Larabawa ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, idan kasar Qatar ta yi watsi da ikon daukar bakuncin gudanar da gasar, watakila za a warware rikicin yanke huldar diplomasiyya dake shafar ta. Wannan ne karo na farko da kasar da ta yanke huldar diplomasiyya da Qatar ta hada rikicin yanke huldar diplomasiyya da ikon daukar bakuncin gudanar da gasar cin kofin duniya.

Kasashe hudu ciki har da Saudiyya sun sanar da yanke huldar diplomasiyya da kasar Qatar domin Qatar din ta nuna goyon baya ga ta'addanci da kawo illa ga tsaron yankin a watan Yuni na bana, daga baya kuma, wasu kasashe na daban sun sanar da yanke huldar diplomasiyya da kasar Qatar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China