in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori a Sudan ta kudu sun amince za su tuntubi junansu
2017-10-12 10:27:33 cri

Wani babban jami'i a Sudan ta kudu ya bayyana cewa, bangarori daban daban dake kunshe a gwamnatin hadin kan kasar (TGoNU), sun amince za su shiga tattaunawar sulhu don wanzar da zaman lafiya wadda ake sa ran gudanarwa a nan gaba a kasar, taron tuntubar wanda kungiyar ci gaban gwamnatocin kasashen gabashin Afrika (IGAD) take son shiryawa.

Michael Makuei, ministan yada labarai na kasar ya fada a Juba cewa, dama sun karbi wata wasika daga kungiyar ta IGAD game da batun sabunta yarjejeniyar sulhu tsakanin bangarorin kasar, ya ce sun riga sun amince a matsayinsu na gwamnatin hadin kan kasa wato TGoNU.

Wannan mataki ya zo ne bayan kiran farko da Dhieu Mathok, babban mamba a kungiyar 'yan adawa ta SPLM-IO karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasar na farko Taban Deng Gai ya yi, inda ya bukaci a samu tuntubar juna a tsakanin bangarorin maimakon haifar da rarrabuwar kawuna.

Babban taron dandanlin don sabunta yarjejeniyar na IGAD, ana sa ran gudanar da shi ne tsakanin ranar 13 zuwa 17 ga watan nan na Oktoba, wanda aka kaddamar da shi a watan Yuni, da nufin sake farfado da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma bayan da aka samu barkewar sabon tashin hankali a watan Yulin bara, tsakanin kungiyar 'yan tawayen na SPLA-IO wanda tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ke jagoranta da wasu sabbin kungiyoyin 'yan tawaye masu dauke da makamai. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China