in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce ta'ammali da kudade ta haramtattun hanyoyi a Afrika zai iya haifar da cikas wajen cimma nasarar shirin SDGs
2017-10-12 09:35:17 cri
Jami'in MDD ya bayyana cewa yin ta'ammali da kudade ta haramtattun hanyoyi zai iya haifar da tarnaki wajen cimma nasarar shirin nan na samar da dawwamamman cigaba duniya wato SDGs nan da shekarar 2030.

Aida Opoku-Mensah, wakili na musamman mai kula da shirin SDGs a Afrika, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, nahiyar tana tafka hasarar kusan dala biliyan 50 na kudaden haraji a duk shekara.

Opoku-Mensah, ya bayyana a lokacin taron kasashen Afrika game da yadda za'a shawo kan matsalar ta'ammali da kudaden haram da na haraji karo na 5 na shekarar 2017, ya ce wannan matsalar tana ci gaba da gurgunta yunkurin kasashen Afrika na samar da kudaden da za'a yi amfani da su wajen aiwatar da shirin na SDGs.

Taron na wuni biyu ya kunshi kwararrun masu tsara dabaru, da wakilan kungiyoyin fararen hula daga nahiyar, inda suka nazarci matakan da za'a dauka wajen dakile matsalar ta'ammali da kudaden ba bisa ka'ida ba a nahiyar ta Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China