in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta hukunta manyan jami'ai sama da dubu 6 bisa zargin cin hanci
2017-10-10 20:14:09 cri

Kwamitin ladaftarwa na JKS ya bayyana a yau Talata cewa, a cikin watan Satumban da ya gabata ya hukunta manyan jami'an kasar kimanin 6,187 bisa zarginsu na keta dokokin jam'iyyar.

A cewar kwamitin sa ido na kwamitin tsakiya na JKS, an samu manyan jami'an ne da aikata laifuffukan da suka sabawa ka'idojin jam'iyyar kusan 4,506. Baki daya manyan jami'ai 47,005 ne aka samu da aikata laiffufuka 33,471, inda aka hukuntasu a watanni tara na farkon wannan shekara da muke ciki.

Wadannan laifuffukan sun hada da bayar da alawus-alawus ko kudin bonus da suka sabawa doka, biyo bayan karba ko bayar da kyaututta da kuma amfani da motocin hukuma ba bisa ka'ida ba.

A karshen shekarar 2012 ne kwamitin ladaftarwar na JKS ya fitar da wasu dokoki guda 8 a wani mataki na rage ayyukan da jami'ai ke aikatawa wadanda suka sabawa doka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China