in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci a gudanar da zaben Liberia cikin kwanciyar hankali
2017-10-10 10:03:07 cri

Shugaban hukumar tarayyar Afrika AU Moussa Faki Mahamat, ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki cikin siyasar Liberia, su tabbatar da gudanar sahihin zabe mai cike da adalci da kwanciyar hankali, a daidai lokacin da kasar ke tunkarar babban zabe a yau Talata 10 ga wata.

Wata sanarwar da tarayyar ta fitar, ta ruwaito shugaban na bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da yakin neman zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Moussa Faki Mahamat ya kuma yi kira ga dukkan al'ummar kasar, musamman shugabannin jam'iyyun siyasa da magoya bayansu, su tunkari zaben na shugaban kasa da na 'yan majalisar wakilai da irin wancan yanayi na hakuri da juna.

Ya kuma bukaci hukumar zaben kasar ta tabbatar da adalci ba tare da nuna fifiko ga wani bangare ba, domin ba da tabbacin hallaci da samun karbuwar sakamakon zaben.

Shugaban ya kuma jadadda kudurin AU na mara baya ga tsarin mika mulki mai cike da tarihi a Liberia, wanda ke da nufin karfafa tsarin demokradiyya da zaman lafiya, wadanda su ne tubalin samun dawwamammen ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China