in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Sanda: Hatsarin mota da ya auku a wajen gidan adana kayan tarihi na London ba shi da alaka da ta'addanci
2017-10-08 12:44:03 cri
Rundunar 'yan sandan Birtaniya, ta nesanta batun ta'addanci da hatsarin da ya auku jiya a birnin London, inda wata mota ta kutsa cikin jama'a dake tafiya a kafa tare da jikkata mutane 11 a wajen gidan adana kayan tarihi na kasar dake birnin.

Rundunar 'yan sandan birnin ta ce an kama mutum 1 bayan aukuwar hatsarin.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce al'amarin batu ne da ya shafi ka'idojin titi, kuma ba shi da alaka da ta'addanci, ta na mai cewa ana ci gaba da bincike.

Ta ce mutane 11 ne aka samu a wajen da raunaka daban-daban, kuma tuni an kai 9 daga cikinsu asibiti, ciki har da mutumin da aka tsare.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, raunakan da mutanen suka samu ba masu ta da hankali ba ne. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China