in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Saudiya da Rasha sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin da suka kai dala biliyan 2
2017-10-06 12:31:31 cri
Rahotanni daga fadar Kremlin ta kasar Rasha na cewa, Rasha da Saudiya sun sanya sannu kan wasu yarjejeniyoyi da darajarsu ta kai a kalla dala biliyan 2.1, yayin ziyarar da sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiya ya kai ziyara kasar ta Rasha.

Wata sanarwa da fadar ta Krelim ta fitar ta bayyana cewa, asusun zuba jari na kasar Saudiya(PIF), da kamfanin mai na kasar mai suna Saudi Aramco da asusun zuba jari na kasar Rasha(RDIF) ne suka sanya hannu kan wadannan yarjejeniyoyi, da nufin kafa wani asusun zuba jari a bangaren makamashi na tsabar kudi dala biliyan 1.

Bugu da kari, hukumomin kasashen biyu, sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa a fannonin binciken sararin samaniya, watsa labarai da sadarwa, cinikayya da tattalin arziki, musamman ayyukan sarrafa mai da kimiyya da fasahar kere-kere da kuma aikin gona.

Sarki Salman da shugaba Putin na Rasha sun kuma tattauna batun hadin gwiwa a fannonin cinikayya da zuba jari da al'adu da bangarorin jin kai da batutuwan kasa da kasa.

Wannan shi ne karon farko da wani sarki mai ci a kasar ta Saudiya ya ziyarci kasar Rasha, tun bayan da aka kafa kasar da ke yankin gabas ta tsakiya a shekarar 1926.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China