in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na OECD ya bukaci a samar da nagartattun hanyoyin lalubo damarmakin kasuwanci a Afrika
2017-10-05 12:29:04 cri
Sakatare Janar na kungiyar kawancen raya tattalin arziki ta OECD Angel Gurria, ya yi kira da a samar da nagartattun hanyoyin lalubo damarmakin kasuwanci a Afrika, wanda shi ne babban jigo wajen inganta bangaren masana'antu.

Da yake jawabi yayin taron kasa da kasa na 17 kan tattalin arzikin Afrika da aka shirya a birnin Paris, Angel Gurria ya ce ba dukkan 'yan kasuwar nahiyar ne ke samun damar amfani da ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata ba, yayin da kananan kamfanonin kasar dake da kasa da ma'aikata 20 ke samar da kashi 22 % na sabbin guraben ayyuka.

Ya kuma bukaci a samar da ingantattun dabaru na magance rashin ka'ida da abubuwan da ke wa dammamakin kasuwanci ga matasa shinge, inda ya kara da cewa, akwai bukatar a taimakawa mata cikin harkokin kasuwancin.

Hukumar tarayyar Afrika da hadin gwiwar kungiyar OECD ne suka shirya taron kasa da kasa karo na 17 kan tattalin arzikin Afrika da ya gudana jiya Laraba domin tattauna hanyoyin inganta kasuwanci da ayyukan masana'antu a Afrika. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China