in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cuba ta yi tir da korar wasu jami'an diflomasiyyarta 15 da Amurka ta yi
2017-10-04 12:35:34 cri
Jiya Talata da maraice ne, ministan harkokin wajen kasar Cuba, Bruno Rodríguez Parrilla, ya nuna matukar takaicinsa, gami da yin Allah wadai da korar wasu jami'an diflomasiyyar Cuba guda 15 da kasar Amurka ta yi, inda ya ce, wannan abun da Amurka ta yi, ko kadan bai dace ba, kuma hakan zai kawo tsaiko ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A yayin taron manema labarai da ma'aikatar harkokin wajen Cuba ta shirya, Bruno Rodríguez Parrilla ya bayyana cewa, Amurka ta yanke wannan shawara ce ba tare da yin tunani sosai a kai ba. Tun a watan Mayun shekarar da muke ciki ne, Amurka ta kori wasu jami'an diflomasiyyar Cuba guda biyu daga cikin kasarta.

Mista Rodríguez ya kuma ce, gwamnatin Cuba ba ta amince da duk wani zargin da Amurka ta yi mata na cewar, wai Cuba ta yi amfani da nau'rar da ka iya kawo matsalar ji ga jami'an diflomasiyyarta. Rodríguez ya jaddada cewa, Cuba ba ta taba kai hari kan jami'an diflomasiyya ko dangoginsu ba, kuma sam ba za ta yi haka ba. Har wa yau, Cuba ba za ta yarda wasu mutane ko kasashe su kai irin wannan hari a cikin kasar ba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China