A cikin wata sanarwar da aka fitar, Tillerson ya ce, Amurka ta yanke wannan shawara ce saboda kasar Cuba ta kasa daukar matakan da suka dace wajen kare lafiyar jami'an diflomasiyyar Amurka dake aiki a kasarta. Amma Tillerson ya yi nuni da cewa, Amurka za ta ci gaba da kiyaye huldar jakadanci dake tsakaninta da Cuba, kana, za ta ci gaba da hada kai tare da Cuba domin gudanar da bincike kan wannan batu.
Tuni a ranar 29 ga watan Satumba ne, Rex Tillerson ya sanar da cewa, sakamakon rashin lafiyar da wasu ma'aikata 21 a ofishin jakadancin Amurka dake Cuba suke ce suna fama ita, Amurka ta yanke shawarar janye wasu ma'aikatan da ba su zama wajibi da kuma dangoginsu.(Murtala Zhang)