in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda a Las Vegas sun ce yawan wadanda suka rasu sakamakon harin ranar Lahadi ya kai mutum 59
2017-10-03 12:58:51 cri
Rundunar 'yan sanda a Las Vegas da ke jihar Nevada ta kasar Amurka, ta bayyana cewa ya zuwa yanzu, yawan mutane da suka rasu, sakamakon harbin kan mai uwa da wabi da wani mutum yayi, a wani fili da ake bikin kade kade a daren ranar Lahadi, ya kai mutum a kalla 59, baya ga wasu sama da 500 da suka jikkata.

'Yan sanda sun ce maharin mai shekaru 64 da haihuwa mai suna Stephen Craig Paddock, ya bude wuta kan mahalarta bikin kada kaden da yawan su ya kai sama da 22,000, daga wani daki dake hawa na 32, na wani otel mai makwaftaka da wurin da ake bikin. Sai dai 'yan sanda sun ce suna da tabbacin mutumin shi kadai ya kitsa wannan ta'asa, ko da yake ba a tantance dalilin sa na aikata hakan ba.

Duk dai da cewa kungiyar IS ta ce ita ke da alhakin shirya harin, mahukuntan Amurka sun ce, ba wata shaida dake tabbatar da alakar maharin da wata kungiya ta 'yan ta'adda.

A wani ci gaban kuma, babban magatakardar MDD ya bayyana matukar kaduwa da aukuwar harin na Las Vegas. A ta bakin mataimakin kakakinsa Farhan Haq, Mr. Antonio Guterres zai rubuta wata takardar ta'aziyya ta musamman ga gwamnatin Amurka, bisa rasa rayuka da wannan hari ya sabbaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China